1) Mu tashi tsaye, dukan ƴan yakin giciye, Mu ta da tuta bisa domin a gan ta dai. A cikin yaƙin gaskiya, Yesu zai bishe mu kuwa Ba za mu koma ba fa, sai gaba za mu yi. 2) Mu tashi tsaye duka, biyayya za mu yi Ga Yesu, Shugabanmu, a cikin yaƙinsa. Ku mazaje ku tashi, ku yi da ƙarfin hali, Ko tsoro ko ragwanci, ba damar wannan fa! 3) Mu tashi tsaye duka, a cikin ikonsa. A cikin ikon kanmu, ba za mu isa ba. Mu tafi da bishara, mu yi ta yin addu'a. Ta wurin bangaskiya za mu ci nasara.Kaa Nami Úžasný Pán Misrga kelding yạ yswʿ ạ̉nt ʿly̱ ạlṣlyb For hvor to eller tre er samlet Gémissant sous l'esclavage Wonderful Way 주님 곁으로 Küçük Bebek Musa My Faith Looks Up To Thee
Song not available - connect to internet to try again?