1) Mu ƙanƙananan yara ne, Ba ƙarfi fa, ba gwaninta. Me za mu yi domin Yesu, Maɗaukaki, mai girma? 2) Mun sani masu tsarki Sun ba da ransu dominsa. Masu aminci, tsarkaka, Sun jure tsananin wuta. 3) Kaddararmu da tasu ɗaya, Mu kuwa muna yin wa'adi, Za mu bi su har mutuwa Don Yesu, haka za mu yi. 4) Kowace rana Masu Bi Wajibinmu ne za mu yi, Mu kashe mugun tunani, Mu hana aikin zunubi. 5) Loton da mu ke yin fushi, Ko mutane sun zage mu, Ko waɗansu sun dame mu, Ko alfarma ta cika mu, 6) A loton nan mu tuna fa, Mu amsa su da haƙuri, Maganarmu da ladabi Don yaƙin Ubangiji ne. 7) Murmushi na salama kuwa Ya haskaka fuskokinmu. Mu yi kome domin Yesu, Mu ƙaunaci jama'armu. 8) Kome ƙanƙantar yara fa, Sun iya ɗaukar giciyensu. Aikinsu daidai ƙarfinsu, Su yi kome domin Yesuفوق العالي عالي Викаме към Христа Throne Room Esti necuprins de timp și spațiu Tan cerca del reino Шаг вперед Har kuni ibodat qilaman علمني أعرفك บัลลังก์ของข้า (ข้าจะก้มกราบบูชา...) ما أعظم الجود الذي ذخرته
Song not available - connect to internet to try again?