1) Mugun bawa nake, na bar tafarkin Allahna. Na ƙi Ubangiji da ɗansa Yesu, na bi Shaiɗan na ƙi Allah . Na shigo duniya da shan giya da yin maye. Ina yin tsammani ina jin daɗi ina yanga da mugunta . Ina zuwa Church ina baiko ina zakka, Amma Ubangiji ba zai sani ba, ranar ƙarshe zan sha kunya. KORUS Wannan abin tausayi ne [Maza: "abin tausayi ne."] Ya isa ma in yi kuka [Maza: "Yi kuka ga Allah."] Waiyo Allah Uba waiyo Allah gani mugun bawa na lalace. Uba ka karɓe ni gani wurinka oh ya Uba ka yi jinƙai. 2) Mugun bawa nake ni ne babban munafiki . Ni mai adalci gaban mutane amma cikina da daci. In ana wa'azi sai in yi kamar na damu. Amma in an gama an komo gida sai in koma bayan gari. To, Ubangijina ni ban bar zuwa gunka ba, Amma na ƙi bari ayyukan duhu ranar ƙarshe babu bege. Korus 3) Mu masu bin Yesu kada mu yi ruɗin kanmu. Gama Ubangiji ba wawa ba ne ba a yi masa ba'a ba. Abin da na shuka shi ne abin da zan girba. Na san hukuncinsa ai babu shakka ranar ƙarshe zan sha kunya. Oh, masu bin Yesu kullum sai ku tuna da ni, Cikin addu'arku gama na zama mugun bawa na lalace. KorusAngel Vamte Tawh ! Я не достоин Ani de indurari كېلىڭ، دوستلار، كېلىڭلار! Libero sei Venid, Pastorcitos بىرگە ٴان ايتىپ، قول شاپالاقتاڭدار Yet Before We See Your Plans 每一天我都需要你的 جاز في نفسي سيف
Song not available - connect to internet to try again?