1) Muna tafiya yau cikin hanyar Yesu. Amma ba mu kaɗai ba ne fa. Yesu ma yana nan, yana tare da mu, Gama shi yana ja gabanmu. KORUS Kai dai ka zo, ka je tare da mu, Cikin hanyar Mai Ceto, zuwa wurin Allah 2) Cikin ƙuncinmu duk, ya kan tallafe mu, Yana ƙarfafa zukatanmu. Ko jaraba ta zo, zai yi hanyar tsira, Masu Bi duk su ci nasara. Korus 3) Da abinci mai rai cikin Maganarsa Ya kan ciyad da kowannenmu, Kamar maƃulƃulai na ruwa mai rai Ruhunsa yana cikinmu duk. Korus 4) Ya yi alkawari, za ya ji roƙonmu, In mun yi cikin sunan Yesu. Sai mu ƙaunace shi, mu bi dokokinsa, Sai mu bi shi da zuci ya ɗaya. Korusمينۋسوۆكا ۔ قىمباتسىڭ سەن 11 Nádherný (Lovely Lord) Шум дождя Отдавна все Исусу съм предал Я не боюсь kẖdẖny lʿlạk Uzak Bir Tepede Pürüzlü Bir Haç Var سۉيۉۉ ۔ بۇل جارىق كۉن، جارقىتات جۉزدۅردۉ Preghiera Marilah, Pujilah Allah
Song not available - connect to internet to try again?