1) Mutane sun fara yawaita a duniya, Sun cika ƙasashe daga gabas har da yamma, Kowa da sunansa da harshe dabam-dabam, Sun bi ta hanyar duniya, sun mance da Uban. KORUS-1 Zan hallakada duniya, In ji Ubangiji, Zan aiki ruwan sama Cikin wannan kwanaki. 2) Duk tunani da shawara ƴan Adam lala ne, Ba wanda ya kula da abin da Allah ya ce, "Na tuba da na yi mutum da dukan masu rai. Zan shafe su da dabbobi har dukan tsuntsaye." Korus-1 3) Akwai mutum, sunansa Nuhu, mai adalci ne, Ya sami tagomashi a gaban Ubangiji, Kullum yana tafiya tare da Allah ne, Tare da shi Allah ya yi babban alkawali. KORUS-2 Ka shiga cikin jirgi, Da kai da ƴaƴanka, Zan hallakada duniya Da ruwan tufana. 4) Shakara ɗari biyu Nuhu ya yi ta wa'azi Ya yi ta shirya jirgi ko bai gane da abin, Mutane sun yi dariya. "Ya hauka" duk sun ce, Amma Nuhu bai kula ba, biyayya shi ke dai. Korus-2 5) Nuhu ya biɗa bisashe da tsuntsaye biyu biyu, Sun shiga cikin jirgin nan tare da ƴaƴansa, Allah ya rufe ƙofa, ruwan tsufana ya zo, Ya rufe fuskar duniya har dukan duwatsu. KORUS-3 Mutane duk sun mutu, Don ba su tuba ba, Amma ya ceci Nuhu Don ya bada gaskiya. 6) Ku mutane ku saurara abin da ya faru, Ku juyo daga duhunku, ku tuba tun yanzu, Ku shiga cikin ƙamnar Yesu, roƙi gafara, Allah za ya ji ku, za ya buɗe ƙofa kuwa. KORUS-4 Ku shiga cikin jirgi, Bai rufe ƙofa ba, Amma idan kun kira Lalle za ku yi makara.Guds ord gir oss løfter Porque el Señor todopoderoso reina Bırakmazsın إلقاء 10 Als wächter في الأعماق Tu es Dieu au-dessus de la terre Ісусе, Ти достойний Рождество Кутсал Китап Танръ'дандър
Song not available - connect to internet to try again?