1) Na ji kiranka, ya Mai Cetona, Na ji zancen ƙaunarka, Da gafararka daga zunubi Da ka yi dominmu duk. KORUS I, zan bi ka, ya Mai Cetona, Zan dai kama hanyarka, Yau na zo wurinka domin gafara, Sai ka ji roƙona yau. 2) Na gaji da bin hanyoyin Shaiɗan Na gaji da bautarsa, Ba ya kyauta wa masu binsa fa, Mutuwa ce ladansa. Korus 3) Ina neman murna da kwanciyar rai, Ina neman gafara, Ban same su ba cikin duniya Sai a wurinka kaɗai. Korus 4) Duk wahalar duniya da zafinta Wanda Masu Bi ke ji, Ba ya kai ga bege na daraja Wanda ya ke cikinka. Korussẖkwn ạ̉nạ yạrby tạ̉ml 3 Avivanos Senor Pri dverách chrámu Credo عمرها ما هاتكون ყოვლისშემძლე ღმერთი Посмотри на крест Chodím vírou في منزل وسط الجليل
Song not available - connect to internet to try again?