1) Na sami ceto ta wurin Yesu. Shi ne Ɗan Ragon da Allah ya bayar Domin ya mutu saboda mu, Mu sami pansarmu wurinsa. KORUS Ceto na Allah kyauta ne Ceto na Allah kyauta ne. Yesu Mai Ceto, Alhamdu ga Allah, I, Ceto na Allah kyauta ne. 2) Na yi ƙoƙari in sami ceto Cikin ayyukan da jiki ke yi, Ni dai na kasa, duk banza ne. Ai, ceto na Allah kyauta ne. Korus 3) Ran da na tuba na sami ceto, Yesu ya yafe duk zunubaina, Na sami rai na har abada, Bukata ta biya, an cece ni. Korus 4) Duk ƴanuwana, ku zo wurinsa, Yau sai ku tuba, ku karƃi Yesu, Bar neman ceto gun ayyuka Don ceto na Allah kyauta ne. KorusGran maravilla es que Jesús Il sacrificio بابا نويل .. بابا نويل Duch a nevesta Sois heureux Всего на миг свой бег остановлю C'est toi V tebe slabý Земля как пустыня A te Gesù
Song not available - connect to internet to try again?