1) Na ta da idona wurin Mai Cetona, Wurin Yesu. Na bata hanya fa, na faɗa jaraba, Sai ka ji roƙona, Mai Cetona. 2) Na faɗi laifina, na faɗi aibina Wurin Yesu. Zuciyata mai dauɗa, ka iya wankewa. Sai ka ji roƙona, Mai Gafara. 3) Shugabance ni dai a wannan duniya, Ina addu'a. Kwaɗayin zuciyata ya kawo jaraba. Ka iya gyartawa, Mai Cetona. 4) A ranar mutuwa, sai ka bishe ni kuwa Har Sama can. Saboda giciyenka, ina da fansata, Nan gaba na yarda in bi Yesu.gẖạly ʿlyk Ohular تراك 7 Сана Хайранъм Come Now Is the Time to Worship Не любите мира ни того что в мире Bůh je má píseň Ты Посмотри Боже я искал веселье dy msẖ ḥạjh ṣʿbh
Song not available - connect to internet to try again?