1) Ni Allahnka ne, Ubangijinka, Ba za ka shiga bautar wani ba. Gare ni za ka dogara kaɗai, Ni ma zan kiyaye ka zuwa rai 2) Ba za ka yi wa kanka sura ba, Sura ta sama ko ta duniya. Ba za ka yi musu sujada ba, Ni, Ubangiji, za ka bauta wa. 3) Ba za ka ƃāta sunan Allah ba, Ba za ka gama shi da ƙarya ba, Amma a cikin duk bukatarka Yi roƙo fa tare da godiya. 4) Ka tuna da rana mai tsarki, Cikinta za ka daina aikinka. Sai dai ka tuna da maganata, Ka nemi ceton ƴanuwanka kuwa. 5) Uba da uwa za ka girmama, Maganarsu ba za ka raina ba. Biyayya za ka yi gare su kuwa, Ni ma zan sa maka albarkata. 6) Kisa ba za ka yi shi ba lalle. Ba za ka ɗauko fansa ba daɗai. Ba za ka ƙi wanda ya ƙi ka ba, Ƙaunarsa za ka yi har abada. 7) Zina da fasikanci za ka ƙi, Kada ka ko yi tunaninsu fa. Sai ka yi zamanka da tsabtar rai, Kiyaye aurenka da tsarkin rai. 8) Kada ka yi sata ko yaudara. Ba za ka ƙwace kayan kowa ba, Amma ka yi aiki da hannunka, Ka riƙa taimakon matsiyata. 9) Kada ka yi wa kowa shaidar zur. Shaiɗan ne uban masu ƙarya, Tsegumi da makirci nasa ne, Dukansu dole za ka ƙi sosai. 10) Kada ka yi ƙyashin kayan mutum. Kada ka nemi mata tasa kuwa. Yi aikin ƙauna da makusanta, Yadda kai ka ke so a yi maka.Per l'abbondanza del tuo amor Жавоб бер менга Раббим! This is the way we wash our clothes/ Here we go 'round the Mulberry Bush Последнее время องค์พระเจ้าผู้ทรงสร้างฟ้าสวรรค์ ยุคสุดท้าย 主啊清晨我寻求你 mhmạ ymr ạlzmạn С чем мне сравнить صابر مع ربي
Song not available - connect to internet to try again?