KORUS Oh duniya, oh duniya, runfar kara take fa. Oh duniya, oh duniya, duniya mai shuɗewa. 1) Zaman duniya, zaman duniya, duniya sai iyawa. Ka jingina ga duniya, sai ƙarewa za ta yi. Korus 2) Ga masu bi na shan daɗi, sun manta da Allahnsu. Ba addu'a, ba wa'azi, ai Shaiɗan ya ɗaure su. Korus 3) Ga masu bi da arziki, sun maida shi Allahnsu. Ga masu bi sun sami illimi, sun maida shi Allahnsu. Korus 4) Ga masu bi, sun sami girma, sun maida shi Allahnsu. Ba addu'a ba wa'azi, ai Shaiɗan ya ɗaure su. Korus 5) Mu masu bi mu lura fa, ranan nan na zuwa fa. Mu farfaɗo mu yi addu'a, biyayya ce za mu yi. Korus 6) Kuɗi, girma, yabo, daɗi, ba za su cece mu ba. Nemi Allah ba shi girma, shi fa zai bada ceto. KorusTví jsme my Спаситель о мне недостойном печется W żłobie leży Магтаал хөөрөг Rab Tanrımız snyn btmr 回想耶稣在世上 Isuse scump lumina vieţii noastre Moneipa Aw! 主必在旷野给你开一条路
Song not available - connect to internet to try again?