1) Ranan nan da ka bayar ta faɗi, Kai ne ka sa duhu ya yi. Mu rera waƙoƙi gare ka, Yabonka kuwa zai tsarkake mu. 2) Mun gode don Ekklesiyarka, Da himma ta ke shaidarka, Tana kuwa kiwon dukan duniya, Ba ta da hutu, ko kaɗan. 3) A ƙasashen duniya dayawa, Hasken safe 'na ƃullowa, Addu'a ba ta fasawa, Yabo gare ka kullayaumin. 4) Loton da mu ke barci fa, Waɗansu su ke farkawa, Kowane lokaci, ƴaƴanka Yabonka su ke furtawa. 5) Mulkinka ba zai shuɗe ba Kamar su mulkokin duniya, Amma ya tabbata da iko, Har kowa ya bi nufinka.Allahı Sәslәyirәm The Love of God Халелуя Il mio Gesù It's Your Love Ty si vzduch čo dýcham Бүтээгч Эзэн (Ямар баян хангай нутаг вэ) أستيقظي امجد الايات غنوا Gel Kalbimi Isıt
Song not available - connect to internet to try again?