1) Ranan nan da ka bayar ta faɗi, Kai ne ka sa duhu ya yi. Mu rera waƙoƙi gare ka, Yabonka kuwa zai tsarkake mu. 2) Mun gode don Ekklesiyarka, Da himma ta ke shaidarka, Tana kuwa kiwon dukan duniya, Ba ta da hutu, ko kaɗan. 3) A ƙasashen duniya dayawa, Hasken safe 'na ƃullowa, Addu'a ba ta fasawa, Yabo gare ka kullayaumin. 4) Loton da mu ke barci fa, Waɗansu su ke farkawa, Kowane lokaci, ƴaƴanka Yabonka su ke furtawa. 5) Mulkinka ba zai shuɗe ba Kamar su mulkokin duniya, Amma ya tabbata da iko, Har kowa ya bi nufinka.Радуйся небо звезды ликуйте ангелы пойте جايلك احمل الصليب Louons le Seigneur ensemble bạlʿz ạ̉mr yǒu yī gè rén shēng lái shì xiā yǎn Spójrz tam w górze qdws qdws qdws Шалом мои друзья Այնքան քաղցր ես այնքան բարի Cœur de Père
Song not available - connect to internet to try again?