1)Ruhun iko, zo gare mu, Mun ga kasawarmu yau. Rashin jinƙai, rashin ƙauna Rashin musun kanmu ma. KORUS Sai ka zo, ka tsarkake mu Daga dukan kasawa. Muna jira, muna jira, Tsarkake mu duk yanzu. 2) Ruhun sani, zo gare mu, Akwai duhu cikinmu. Sanasshe mu, koya mana Hanyar tsarkakewar rai. Korus 3) Ruhun wuta, zo gare mu, Kone duk muguntarmu Har mu zama mutanenka Cikin dukan gaskiya. Korus 4) Ruhun haske da addu'a, Bi da mu, ka ƙarfafa. Muna bege, muna bege Har mu sami nasara. Korus 5) Ruhun ƙauna, zo gare mu, Sai ka yafe mu yanzu. Muna jira, muna kuka, Amsa dai addu'armu. Korus 6) Ƴanuwa, ku yafa Yesu, Yafa sabon hali kuwa. Yafa kuma zuciyar tausayi, Ladabi da jurewa. Korus 7) Ruhun Kristi, ni na gode, Kana nan a zuclya, Mallake ni, mallake ni Daga yau har abada. KorusUnknown Prišli sme s chválou Теңирим, кечир мени Йеңи келишим Incrociare un po' le mani fkẖr ạlknysh wjmạlhạ sydhạ ạlmsyḥ طلبتي ربي اجعلني أشبه Chci zářit Jak dobré je vzývat jméno Tvé
Song not available - connect to internet to try again?