1) Wannan bishara kuwa ta mulki Za'ayi wa'azinta ga duniya. Domin shaida ga dukan al'ummai Sa'annan mutuƙa za ta zo. KORUS Sa'annan, sa'annan, matuƙa, matuƙa Sa'annan matuƙa za ta zo. 2) Gama kamar walƙiya daga gabas Kuna ganinta kuwa bar yamma. Haka nan Ɗan mutum za ya zo. Sa'annan mutuƙa za ta zo. Korus 3) Daga itacen ɓaure ku ga ne Sai ku koyi misalinsa Sa'anda yana hudo ganyensa Sa'annan mutuƙa za ta zo. Korus 4) Ku tuna da zamanin Nuhu ƴan'uwa Ya sha ba'a cikin aikinsa Amma ya ci gaba da yin jirginsa Sa'annan matuƙarsu ta zo. Korus 5) Sai mu jimre da aikin bishara Har dukan duniya ta tsira Domin Yesunmu yana zuwa Sa'annan matuƙa za ta zo. Korus 6) Yesu zai karɓe mu cikin sama. Cikin gidan Ubansa. Rawanin Rai yana jiranmu. Sa'annan matuƙa za ta zo.Sevaman deysan Eu nu ma tem, eu nu ma tem كەلشى، كەلشى يمانۋيل В сегодняшнюю ночь звезда любви явилась Alleluia al Re Мой Покровитель Рəббим - О диридир День ночь дожди метели Верю я в Тебя (Бог творящий чудеса) Je veux te louer
Song not available - connect to internet to try again?