An haife shi cikin Yahudiya wata ran.
Cikin zamaninsa, Allah ne ya sa
Mutanensa su horu a ƙasar magauta.
Tsoron Ubangiji farkon ilmi ne,
Sai mu tsaya kamar yadda Daniel ya yi.
Aka gabatad da shi ya zama sananne.
Cikin wannan duka, shaida ya ke yi,
Ba ya neman girman kansa, sai na Allahnsa.
Korus
Kunya ba ya taƃa ji a cikin wannan ba.
Can fa wata ra na a ke ƙararsa,
Duk da haka ya yi ta addu'a kamar da.
Korus
Ba su iya buɗe baki ba, balle su ci.
Daniel ya kwana lafiya ƙalau,
Can da safe ya ji muryar sarki, cewa "Zo"
Korus
Har yanzu akwai shi isasshe ne dominka
Kada ka yi shakka, ko ka ji tsoro
Wurin Ubangiji dukan kome ya yiwu.