1) Tafiyarmu a duniya ta kusa ƙarewa. I, kome nisan hanya, lalle ta kai gida. Ko duhu muka ratsa, gari zai waye can. Babu sauran dare kuma gun Immanuel. 2) Da jinƙai duk da ilmi, ya shirya hanyata, Har ko a cikin duhu na iske haskensa. Zan yi yabon Mai Sani, zan yi yabon Mai Yi. Farko ne shi da ƙarshen, shi Immanuel. 3) A zuciyar Almasihu, ƙauna ta yalwata, Ta fi ta duniva daɗi, kome ne daɗinta. Can Sama dai zan gane alamun ƙaunarsa. Bisa goshina sunansa, Yesu Immanuel. 4) Amarya, idanunta a wajen ango ne, Ai, ba ta duban wani, sai fuskarsa kaɗai. Ni haka, fuskar Yesu da jiki sokakke, Ɗan Rago ne zan duba, shi Immanuel.WE'LL NEVER SAY "GOOD-BYE" Che Tu sia il mio tutto Хүлээсийг тасдана Il profumo della sua conoscenza Иисус мне больше чем весь мир కనుచూపుమేరలోన ఏ Uzumzorda uzum dumaloq dumaloq ạ̉nạ bạʿlnkm zwj wzwjẗ جۉرۅگۉ ىيسانىن تولو مەەرىمگە Не слухай і не вір
Song not available - connect to internet to try again?