1) Tashi, mu gai da Ubangijinmu. Yau aka haife shi da safen nan. Mai Ceton duniya, Ubangiji ne. Ya zo ya ɗauki siffar ɗan Adam. Tashi, mu ji waƙar mala'iku, Ƙaunar Ubangiji ne zancensu. 2) Yabo ga Allahnmu Maɗaukaki, In ji su taron rundunan Sama. An kawo muku yau da daren nan, Bisharar murna zuwa duniya duk. A birnin Dawuda aka haife shi, Mai Ceto, shi ne Almasihunku. 3) Da jin labari, makiyayan nan Sai suka tashi za su wurinsa. A Baitalahmi, ga jaririn nan A kwance dai cikin sakarkari. Sun tashi kuwa, sun ba da shaidarsu Manzannin farko ne na Ɗan Mutum. 4) Mu kuwa da halin ladabi mu ji Labarin haihuwarsa ta ƙanƙanci. Tuna da haifuwarsa da giciyen, Bi sawun Yesunmu da hawaye. Wannan jariri shi ne Ɗan Allah, Ya kau da dukan hakkin zunubi. 5) Cetattu fa ta wurin ƙaunarsa, A gaban kursiyi za mu rusuna. Za mu ga iyakar darajarsa, Za ya bayyana mana ikonsa. An haife shi ta wurin budurwa, Gare shi za mu yi godiya tutur.قۇبانىچ مەنەن تەڭىرگە ىردايبىز Pribeag azi prin lumea de chin şi dureri يا إلهي نادِ قلبي Մեծարում եմ Քեզ Я не боюсь ḥbẗ qsẖ lạnẗ kmạ Baqytty ómir bir Sende Niebezpieczny to stan Non ti lascerò mai
Song not available - connect to internet to try again?