1) Tsakanina da Mai Cetona Ba zan bi ruɗin duniya ba, Na bar nishatsin wannan duniya, Sai dai Yesu ne, ni ke sonsa. KORUS Tsakanina da shi, babu kome Da zai hana in ga fuskarsa. Alherinsa ba zai hannu ba In na tabbatadda zuciyata. 2) Me zai raba ni da Mai Ceto, Ko raɗaɗi da ruɗin Shaiɗan? Duk waɗannan ba zai raba mu ba, Shi ne kaɗai zan manne masa. Korus 3) Ba fahariya ko alfarma, Ko ni kaina ko abokai, Ko da shi ke zan sha tsanani, Duka da haka Shi ni ke so. Korus 4)Ko jaraba ta taso mani Ko duniya tana ƙi ni. Addu'a za ta ba ni nasara. Ba abin da zai hana. Korusانطق على لساني مەنىڭ جۇرەگىم قازىر قۋانىشتى Vocea Lui se aude Прихожу к Тебе я с хвалою 우리 모일 때 Невиновна Nous sommes une maison Smieme kráčať Anjir bargi quriganda ham Nimm mein Herz
Song not available - connect to internet to try again?