1)Tun da farkon hasken safe, Ko ka yi addu'a Cikin sunan Yesu Kristi, Ka yi roƙo har ka sami Taimakonka yau? KORUS Yin addu'a dai zai ba mu Albarka ba iyaka. Sai ka riƙa yin addu'a Kowace sa'a. 2) Lokacin zuwan jaraba, Ko ka yi addu'a Don ka sami ikon Allah, Ruhunsa ya taimake ka Har da nasara? Korus 3) Lokacin da ka ke fushi Ko ka yi addu'a Kada Shaiɗan ya rinjaya Har ya sa ka yin tuntuƃe Cikin fushinka? Korus 4) Cikin tsanani da ba'a Ko ka yi addu'a, Ko ka jure, kana roƙo Har ka sami hutun ranka Cikin Almasihu? KorusՏեսեք Պատերազմ Են Գնում Подай мені руку Qachon xafa bo'lsam Halleluja, denn der Herr unser Gott Тэ миян вежа Ен! Ó, duše, pomni lásky Über die Berge und das Meer fließt dein Liebesstrom zu mir يسوع زي السكر Jeg vil løfte mine hender til Deg Агнец Господень - Иисус
Song not available - connect to internet to try again?