1) Ubangiji Allah, ga mu nan gabanka. Tun da farin hasken safe, mu ke nemanka. Muna yabon sunanka, ya Mai Iko Duka, Muna sujada, ya Mai Tsarki. 2) Ubangiji Uba, kai ne farkon kome, Kai ka ba da Ɗanka Yesu domin cetonmu. Mu da muka tayar, kai ka ji tausayinmu. Muna sujada, ya Mai Tsarki. 3) Ubangiji Yesu, kai ne Almasihu, Kai ka fanshi bayin Shaiɗan daga bautarsa. Kai ka ba da jininka domin mu mutane. Muna sujada, ya Mai Tsarki. 4) Ubangiji Ruhu, sunanka Mai Tsarki, Kai ne kana koya mana hanyar cetonmu. Kai ne jagabanmu, kullum sai mu bi ka. Muna sujada, ya Mai Tsarki. 5) Allah Ubangijinmu, ɗaya cikin uku, Harshe ba ya iya faɗin girman sunanka. Uba, Ɗa, da Ruhu, uku cikin ɗaya, Muna sujada, ya Mai Tsarki.V oku odvahu, smělost Дуйур Бана Севгини Ты разбит и так трудно идти Stratená nájdená Sakin Olur Bilirim Rabsin Нейлейим дюняйъ Ne hale düştün, boynun bükülmüş Se crederai Память моя qlby ạsẖthy̱
Song not available - connect to internet to try again?