1) Ubangiji, ka bishe ni A tafiyata duka. Sai ka ba ni farinciki, Sai ka ba ni bangaskiya, Sai ka yi mini alheri, Sai ka taimake ni yau, Gama ni ban iya kome, Ni kaɗai, a duniya ba. 2) Ubangiji, ka bishe ni A tafiyata duka, Gama a kan jarabce ni, Ni kan shiga tsanani Duk wahala daga Shaiɗan Ta kan dulmayad da ni Gama ni ban iya kome, Ni kaɗai, a duniya ba. 3) Ubangiji, ka bishe ni A tafiyata duka, Gama ilmi ya kan kasa, Ina son hikimarka. Duk ƙoƙarina ya kasa, Sai ka ba ni ƙarfinka Gama ni ban iya kome, Ni kaɗai, a duniya ba. 4) Ubangiji, ka bishe ni A tafiyata duka, Kuma ranar da zan mutu, Sai ka yi ta taimako. Ina so in yi ta shiri Don in tsaya gabanka. Ni kaɗai ban iya zuwa Cikin kwarin mutuwa ba, Ni kaɗai ban iya zuwa Cikin kwarin mutuwa ba.أنا ليك Fede Ráč naše deti sám Już ostatni za górami Как олени к воде весною Чюнкю Нереде Късканчлък Lalpa Isun Ti a Teach me your ways Ákeniń mahabbatynda shomylamyn men Блаженны те кто в доме Твоём
Song not available - connect to internet to try again?