1) Ubanginmu, Mai Ceto, Don zumunta ne muka zo. A duniyan nan sai sakewa, Wurinka fa sai hutawa. 2) Tun jiya, yau, har abada, Madauwami ne sunanka! Kai ne ka kafa duniyan nan, Kai ne mai shirya gida can. 3) Almasihu, Cetonmu, Ba mu da wani taimako, Amma ƙaunarka cikakkiya, Ita ce garkuwar ƴaƴanka. 4) Ƙaunarka ! har wa yau ta tsaya Da, ka ɗanɗana mutuwa. Can bisa kursiyin Allahnmu, Yanzu ka rayu dominmu. 5) Yabo, daraja, godiya Gare ka Yesu Ɗan Allah! Ka cika mu da Ruhunka, Ya koya mana nufinka.Denn der Herr zieht mit uns voran Cariñoso Salvador ليأتِ ملكوتك Světu zaznívá zvěst spásná قۇداي دۉينۅنۉ جاراتقان سۅزۉ مەنەن БОГ СЛЕЗЕ МЕЖДУ НАС Познать Тебя Venite a me Менинг Нурим rby sbyt qlby
Song not available - connect to internet to try again?