1) Wannan labarin Yesu kullum in riƙa ji, Labarinsa mai daɗi, labari ba mai fi. Tuna mini wannan kullum, Mai saurin mantawa ne ni, Labarinsa mai daɗi, labarinsa mai fi. Daɗin labarin Yesu, daɗin labarin Yesu, Daɗin labarin Yesu, kullum in riƙa ji. 2) Idan na faɗa laifi, labarinsa in ji, Labarin fansar ƴan Adam da shi kaɗai ya yi. Idan na ratse hanya wadda ta kai ni rai, In komo kan labarin nan na Yesu mai ba da rai. Wannan labarin Yesu, wannan labarin Yesu, Wannan labarin Yesu, kullum in riƙa ji. 3) Ba ni labarin Yesu, mai zunubi ne ni, Labarinsa mai daɗi, a hankali in ji. Kada in fasa jinsa, labarin ƙaunarsa, Ƙauna mai girma ƙwarai, ƙauna ba iyaka. Ba ni labarin Yesu, ba ni labarin Yesu, Ba ni labarin Yesu, labarin ƙaunarsa.ما دمت ربى في الطريق العىستار ايتىڭدار قۇدايعا، ماداقتاڭدار ٴتاڭىردىڭ ەسىمىن Už mnoho liet أنا في المسيح خليقة جديدة เจ็ดวิธีสรรเสริญพระเจ้า Seven Ways To Praise The Lord There's a Great Day Coming الفترة الرابعة Сээӊ ынакшылыӊ кызыгаары чок Syukur Kupanjatkan สาธุการพระนามวิสุทธิ์
Song not available - connect to internet to try again?