1) Wata rana za mu gan shi, Yesu Ubangijinmu. Za mu tsaya a gabansa Wanda ya ke ƙaunarmu. KORUS Wata rana za mu gan shi Cikin dukan daraja. Za mu yi masa sujada. Za mu duba fuskarsa. 2) Mu dai ba mu ganin Yesu Cikin wannan duniya Amma can a gidan Sama Za mu duba fuskarsa. Korus 3) Ran da muka kai gun Yesu, Shi zai shafe hawaye, Babu sauran ƃacin zuciya, Sai dai murna za mu yi. Korus 4) Za mu gan shi, Halleluya! Za mu ga Mai Cetonmu. Za mu faɗi a gabansa Wanda shi ke Sarkinmu. KorusOta Men Sevaman Планета Мой одинокий путь во тьме лежал Pane, ráč Ty sám! Copilaș bălai cu chip de soare موسيقى أسكن تحت ظل Doamne mai vreau Rusalii Вақте Исо, шоҳи шоҳон, таваллуд шуд дар ин ҷаҳон, Ситораи наҷоти ман медурахшид дар осмон Nelle mani Tue 我有一个心愿
Song not available - connect to internet to try again?