1) Ya Allah, mai ƙauna, Zo, ka kusance mu, Ka duba amarya da angonta. Sun zo su yi wa juna alkawari. Ya Allah, sa albarka, Ka cika su da murna, Ka haɗa su da ƙauna mafificiya. 2) Alkawarin aure Abu ne mai tsarki, Kada su tsinke shi tun suna da rai Ko cikin daɗi ko a cikin ƙunci Ka sa su yi aminci, Ka riƙe su da ƙarfi, Ka ɗaura musu aure mai lafiya. 3) Ya Yesu, mai ƙauna, Ango na Ekklesiya, Kai ne masoyin dukan tsarkaka. Zauna tare da mijin da matarsa, Ka bi da su, ya Yesu, Ka zama Shugabansu, Ka mai da su, ya Yesu, masoyanka.يارب أنت أبونا S láskou يا من تعيش Edifica un pudblo potente Is He Worthy Что я могу Тебе сказать Grazie Signor Я не хочу полуправды ʿạyz ạ̉ḥky lk kạ̉sy fạḍ
Song not available - connect to internet to try again?