1) Ya Allah, miƙa hannunka, ka tsai da haukansu, An kashe Almasihunka ta hannun miyagu. 2) Ba za ka bar Mai Tsarkinka cikin kabari ba. Ba za ka bar maƙiyansa su ci nasara ba. 3) Dā, kayayuwa tsinana sun soki goshinsa. Yanzu ka naɗa Almasihu a hannun damanka. 4) Shi wanda aka kunyata a cikin duniyan nan, Ka tashe shi da daraja, ka ba shi girma can. 5) Shi ne ya mutu dominmu, ya ɗauki giciyensa. Mun sami rai da lafiya ta wurin dūkansa. 6) Idan mun mutu tare nan, mun ɗauki giciyensa, Tare kuwa za mu yi murna a cikin mulkinsa. 7) Ina misalin yabonka, ya Yesu Almasihu? An sanya mulkin kome nan ƙarƙashin sawunka.kly lyk Ямар үг вэ kl mftwḥ ạlʿynyn Әй адәмләр ойғиниңлар Bárimiz birge bolǵanda! La tua maestà Mędrcy świata قل كلمة 찬양해 Imádlak, én Istenem
Song not available - connect to internet to try again?