Ba kai ne ka kira ni ba?
Mai yalwar jinƙai, yafe ni,
Na zo, na zo, ka cece ni.
Alheri, ceto naka ne.
Sai ka ji kukana yanzu,
Na zo, na zo, Mai Cetona.
Ni ne na bata zuciyarka.
A cikin rashin ƙarfina
Na zo, na zo, ka cika ni.
Ƙaunarka ce ta jawo ni,
Ba za ka ƙi mai sonka ba,
Na zo, na zo, ka karƃe ni.