1) Ya Allahnmu Madauwami, Kai ne ka halicci teku, Da koguna da taffukan Da su ke cikin duniya. Ka ji mu don ƴanuwanmu, Da jinƙanka ka dube su. 2) Ka tsare su da ikonka. Idan hadari ya taso, Ko iska ce mai fyaucewa Ta girgiza jiragensu. Ka ji mu, muna roƙonka, Su kai kwata ma lafiya. 3) Mun tuna yadda Almasihu, Ya shiga cikin jirgi da. Ya tsauta wa raƙuman ruwa, Sun kwanta, sun natsu sosai. Ka ji yanzu, ya Almasihu, Ka tsare ƴanuwanmu yau. 4) Ka tsame su da ikonka Daga masifu masu yawa, Su dogara gare ka kuwa, Su sansance amincinka. Dukanmu za mu yabe ka, Ya Allahnmu mai ta'aziyya.E o misiune sfântă Я знаю мама rạjʿ lyk Даже если я по долине тени смертной пойду Dünyanın sonu geliyor Bože, Teba chválime Սուրբ Գահի Առջև Կանգնած Rabbim keldi Փառք Տվեք Աստծուն 내게 있는 모든 것으로
Song not available - connect to internet to try again?