1) Ya Almasihu, ga ni nan, Na zo gare ka ƃatacce. Ba wanda za ya cece ni, Ba taimako, sai kai kaɗai. KORUS Ga ni nan, ga ni nan, Ya Almasihu, ga ni nan. Na zo da kayan zunubi, Ka kau da shi, ka wanke ni. Ga ni nan, ga ni nan, Ya Almasihu, ga ni nan. 2) Ban zo da kuɗin fansa ba, Ba kome nan sai zunubi, Amma na duba jininka, Ka ji tausayi, ka karƃe ni. Korus 3) An gama aikin cetona, Ga jininka ya fanshe ni. Yanzu na zama bawanka, Har abada ni naka ne. KorusБал гиби Иисус живой HE HAS TAKEN ALL MY SINS AWAY Berge mich ЕН КУДРЕТЛЪ ТАНРЪ 神的儿女要有信心的眼 Grato es decir la historia yào bǎ nǐ de zhēn ài chuán biàn كل الأشياء ياللي بتخاف عليا
Song not available - connect to internet to try again?