1) Ya Almasihu, sarkin tsarkakanka, Kai ne ka taya su cikin jaraba. Duk Masu Binka suna yabonka. Halleluya! Halleluya! 2) Kai ne mazauninmu har abada, Kai fā na ceto ne da mai taimako. Kai Shugaba ne cikin yaƙinmu. Halleluya! Halleluya! 3) Idan da tsoro cikin zukatanmu, Ko ikon Shaiɗan ne ya ke ƃata rai, Kai ne ka fi shi, kai kuwa namu ne. Halleluya! Halleluya! 4) Kai ne ka kira mu mu bi bayanka. Kai za ka taya mu cikin yaƙin nan. Shaiɗan, magauci, za ka taka shi. Halleluya! Halleluya ! 5) Sai wata rana sammai za su buɗe, Za ka bayyana nan cikin daraja. Mu kuwa magada ne na muikinka. Halleluya! Halleluya!En Mutlu Gün Сəһрадан Бир Сəс Ҝəлир Сəһрадан جۉرۅگۉمدۅن تابىنىپ Боже, чути Слово อัศจรรย์พระเยซูของเรา Yaşamağa güc ver mənə Liturgia - Kyrie L'horizon se colore Here Comes Heaven يا سيدي إني أطرح نفسي
Song not available - connect to internet to try again?