1) Ya ku ƴanuwa, bar bin duniya, Ta da murya domin Yesu. Yafa makamai, dukansu sosai, Shiga Yaƙin Ubangijinmu. KORUS Tashi zuwa yaƙin Almasihu, Tuƃe nauyin kayan duniya, Gaba dai, ba za mu waiwaya ba, Ubangiji Shugabanmu ne. 2) Kome jaraba, muna cin gaba, Lalle za mu ci nasara. Ikon magauci ba mu raina ba, Amma dai ba za mu bi shi ba. Korus 3) Ubangijinmu, ji addu'armu, Ba bayinka dai ikonka. Muna dogara ga Maganarka, Mu da kanmu ba mu iya ba. Korus 4) In mun gama nan, za mu huta can Gidan Allahnmu har abada. Ladan aikinmu yana jiranmu, In mun yi shi da aminci fa. Korustʿlyq 2 Tek Bir Dostum Var Dobrý je náš Bůh Бютюн Кушлар Хамт Едер మహిమ నీకే, ఘనత నీకే, ప్రభావం, నీకే ప్రభు غير دربك Чун шарорату гуноҳ карда дунёро табоҳ ạ̉nt yạ rb yswʿ ʿznạ wfkẖrnạ Şifa ver ạ̉lạ tʿlmwn
Song not available - connect to internet to try again?