1) Ya Maɗaukaki na Allah, Zan yi yabonka ƙwarai. Kai, ka shafe zunubaina, Kai, ka ba ni sabon rai, Halleluya, Halleluya, Girma duka naka ne. 2) Mun yabe ka don alheri Zuwa kakaninmu da. Yau da gobe ka ke nan fa, Ƙaunarka ta tabbata. Halleluya, Halleluya, Ɗaukaka amincinka, 3) Makiyayi mai tausayi, Wanda ya san halinmu, Daga dukan jarabobi Ya fisshe mu lafiya. Halleluya, Halleluya, Wa ke jinƙai kamarka? 4) Ɗaukaka ga Ubangiji, Kai kaɗai mai adalci, Kai ne farko, kai ne ƙarshe, Ƙauna, Iko, Gaskiya. Halleluya, Halleluya, Mun yi maka sujada.БОГ ЗА НАС ВОЮВА Iso Masih, Dunyo Xoni! Tak Bóg umiłował Келди Раббим mạdẖạ yṣnʿ lkrmy Cadenas romper Emmanuil Teraz w młodych życia latach Tu es le Dieu fidèle hạḥtmy fyk yạrby
Song not available - connect to internet to try again?