1) Ya Mai Ceton duniya duka, Kasa mana kunnenka. Bayinka fa, muna roƙo, Muna neman ikonka. Ba don kanmu mu ke so ba. Ko'ina ga ƴanuwa. Mu mun samu, su sun rasa. Nuna mu su cetonka. 2) Mu da kanmu dai mun kasa, Ikon ceto naka ne. Ban da kai, ya Ubangiji, Aikinmu na banza ne. Ɗibo mana iko naka, Cika mu da ƙarfinka. Kullayaumin taimake mu, Har mu gama aikinka. 3) Inda za mu shiga duka, Taimake mu, bayinka, Domin masu ji su yarda Da labarin ƙaunarka. Ƙarfafa ma'aikatanka, Sa musu albarkarka, Har mutane duk su tsira, Duk su shiga mulkinka.Намайг тас харанхуй Қаны Мәсіхтің శాశ్వతమైనదీ నీతో నాకున్న అనుబంధము THE WAY OF HEAVEN Месих'ин Адънъ Бирликте ЬОвелим! مرنى أن آتى إليك - موسيقي Prosbu našu, Pane čuj 神在作事 Beklecem Benim Allahımı A Stefano
Song not available - connect to internet to try again?