1) Ya Maɗaukaki na Allah, Zan yi yabonka ƙwarai. Kai, ka shafe zunubaina, Kai, ka ba ni sabon rai, Halleluya, Halleluya, Girma duka naka ne. 2) Mun yabe ka don alheri Zuwa kakaninmu da. Yau da gobe ka ke nan fa, Ƙaunarka ta tabbata. Halleluya, Halleluya, Ɗaukaka amincinka, 3) Makiyayi mai tausayi, Wanda ya san halinmu, Daga dukan jarabobi Ya fisshe mu lafiya. Halleluya, Halleluya, Wa ke jinƙai kamarka? 4) Ɗaukaka ga Ubangiji, Kai kaɗai mai adalci, Kai ne farko, kai ne ƙarshe, Ƙauna, Iko, Gaskiya. Halleluya, Halleluya, Mun yi maka sujada.Oltre ogni limite Ey Perişan Canım 稍微不儆醒 ạ̹dẖạ kntm Non posso fare a meno di Te ОТВАРЯМ ОЧИ И ВЗИРАМ СЕ В ТЕБ yạlh mn ḥb ʿjyb Kül Yerine Güzelliğini Ver سألوذ بحضنك yṭlq qlby
Song not available - connect to internet to try again?