1) Ya tsarkaka na Allahnmu, Yanzu kun gama yaƙinku. Kun kwance dukan ɗaurarru, Kun ba da su ga Allahnku. Ya tsarkaka na Allahnmu, Gun Yesu za ku huta yau. 2) Ya tsarkaka na Allahnmu, Kun kai ga burinku yanzu. Ba yunwa, babu ƙishiruwa, Ba wuyar hanya, ba gajiya. Ya tsarkaka na Allahnmu, Yesu ya shirya gidanku. 3) Ya tsarkaka na Allahnmu, Barci ya kwashe jikinku, A ƙarewa Ɗan Allah kuwa Zai raya ku da nasara. Ya tsarkaka na Allahnmu, Ga hasken Yesu wurinku. 4) Ya Allahnmu na tsarkaka, Muna roƙo a wurinka. Albarka ga Ubangiji Da Ruhunsa Mai Tsarki. Ka sada mu da tsarkaka, Ka kai mu wurin zamanka.Je crois Kruin Orrel: Praat ek mense eng'letale Қандай баҳтли Мы будем славить mn ywm mạ qblt Благ наш Господь qlt stạ̉ty Господь Ты мой Бог Это Рождество Иммануил
Song not available - connect to internet to try again?