1) Ya Ubangijinmu, dube mu duk yanzu A gabanka. Sarkin sarakuna, mai iko duka kuwa, Karƃi sujadarmu, Ubangiji. 2) Roƙonka mu ke yi don masu mulkinmu, Ka cece su. Tsawanta ransu kuwa, su ma a zuciyarsu Su nemi fuskarka, Ubangiji. 3) Daidaita hanyarsu cikin sarauta fa, Ka riƙe su. Ba su albarkarka, girma da lafiya, Iko da nasara, Ubangiji. 4) Tuna da ƙasarmu, ka san bukatarmu A duniyan nan. Kai ne Mai Cetonmu, kai ne shugabanmu, Bishe mu duk yanzu, Ubangiji.Yallah Yallah Titok és ajándék Ey Reb Îsa Tu Were День склонился к вечеру Béni sois-tu, tendre Maître! هوذا قد صار ليل مظلم Majestet, Konge i evighet تعالى يا يسوع بيتنا Қасиетті сәби дүниеге келді 敬拜赞美迎来神同在
Song not available - connect to internet to try again?