1) Ya Ubanmu, sa albarka Bisa kan ƴaƴanka yau. Za mu yi yabon sunanka, Addu'a kuma za mu yi. Mun ji labarin Ubangiji Na gaskiya da alheri. Cikin hasken Almasihu Za mu gane ƙaunarka. 2) Maganarka ta koya mana Mu ƙaunaci ƴanuwa, Mu girmama gaskiyarka, Mu yi haƙuri kullum, Mu hori kanmu da aniya Domin mu yi aikin kirki, Loton shiru ko na faɗi, Koyaushe sai kamewa. 3) Bari ruhohinmu duka Su yi yabon ikonka. Murna, ƙauna da salama Su kasance wurinmu duk. Mu zama amintattu naka, Ko cikin aiki ko tunani. Tsakaninmu da ƴanuwanmu, Mu yi duk domin Yesu. 4) Mu ɗaukaka sunan Allah, Mu ambaci duk tsarkinsa. Albarka kuwa ga Almasihu Da Ruhunsa Mai Tsarki. Ga Allah Uba, Allah Ɗa kuwa, Allah Ruhu Mai Tsarki, Mu ha ka dukan daraja ma, Allahnmu har abada.Dicsérettel jövünk eléd Dáváš mi lásku vzácnou На зелёный злачный луг Если б очи веры Боже Dopóki Zbawcę mam Je reviens au cœur Then He Rose Всю истину познать хочу Үзэгтүн Би шинэ зүйлийг хийнэ تكلم يا رب
Song not available - connect to internet to try again?