1) Ya Yesu, kayan adona Jininka ne da giciyenka. Ko duniya dai ta yi gobara, Yafe da waɗannan zan tsaya. KORUS Kan Yesu, Fan Ceto, na tsaya, Ba wani wurin rai, ko ɗaya. Ba wani wurin rai, ko ɗaya. 2) Ko zunubaina sun yi yawa Har ba mai iya ƙirgawa, Ba wanda ba a shafe ba Ran da ka ba da jininka. Korus 3) Dabarun duniya suna nan, Dabarun banza na Shaiɗan. Tawa dabara ɗaya ce, Cetona jinin Yesu ne. Korus 4) Domin shari'ar Lahira, Yesu, na fake wurinka. Ban duba nawa aiki ba, Gare ka ne na dogara. Korus 5) A ƙofar Sama, izinina Sai jininka da giciyenka. Ko gaban kursiyi, murnata Jinin Yesu da ƙaunarsa. Korusİnsan qәlbi Иноят берар 今天今天最好的消息 ạḥkyly ʿly ạlly fy qlbk Не мога без теб Dari V Track 09 Он Христос House of the rising sun O mon âme, exalte et chante! أجيوس
Song not available - connect to internet to try again?