1) Ya Yesu, muna jiranka, Da ikonka na warkarwa. Ba mu da ikon taimako. Ka cika dukanmu yanzu. 2) Ka ji mu, muna nemanka. Ba duk a nan sun san ka ba. Mun sani kana nemansu. Jawo su duk, Mai ƙaunarmu. 3) Kai ne mai sanin cutarmu, Mai gyara mugun tunani. Tone ƃoyayyun laifofi, Mai Fansarmu kan giciye. 4) Ka cire ƙarin mutuwa, Ka kau da aikin maciji. A cikinmu, yi nasara Don mulkinka madauwami. 5) Ka dubi masu ƙunci yau. Rinjayi duk ƴan kangara. Ka kwance ƙangin ɗaurarru, Ka mai da su a hanyarka. 6) Ya Almasihu, Ɗan Mutum, Ka ɗauki tabi'armu da, Alherinka mai yawa ne, Mai Cetonmu, Mai Gafara. 7) Kai ne da ikon warkarwa, Da yau da kullum kamar da. Ka ji mu yau, Maɗaukaki, Warkad da mu da hannunka.Ascribe Igazságban, szellemben อิมมานูเอล Emmanual Тубом Голгофае, выны, Canterò di te Путь на Голгофу Libertà Hosanna Con Cristo en el barco ạlfjr sẖq wlạḥ
Song not available - connect to internet to try again?