1) Ya Yesu, Ruhunka kaɗai zai juye zuciyarmu, Ikonsa ma a cikinmu zai sake halinmu. KORUS Ya Ruhu mai taimako, wurinmu duk ka zo, Ka cika dukan zuciyarmu, ka ba mu ikonka yau. 2) Ya Yesu, Ruhunka kaɗai, zai ba mu ƙaunarka, Ikonsa cikin ranmu kuwa zai juye gurinmu. Korus 3) Ruhunka, Yesu, ƙauna ne, Ruhun bangaskiya kuwa. Shi fid da kwaɗayinmu duk da ikon ƙaunarsa. Korus 4) Ya Ruhun Yesu, muna so ka ji addu'armu, Ka sauko nan da ikonka, ka zauna bisanmu. KorusRy Jehovah Tomposoa DWELLING IN LOVE Zaila'n Awi Hitiu Gdzie się troski ścielą يا رب اسمك أرفعه tiān tiān chàng hā lì lù yà Mirad el gran poder de Dios La mia rocca Všichni žízniví, pojďte k vodám Бимон бо ман Худои меҳрубон
Song not available - connect to internet to try again?