1) Ya Yesunmu, mun taru wurinka. Ka ji roƙonmu, mu ne ƴaƴanka. Ya Ruhun Allah, buɗe zuciyarmu, Yi aikinka, ya Ruhu, cikinmu. 2) Bayyana kanka cikin ƙaunarka. Bishe mu kuwa ta wurin Ruhunka. Mai Taimako fa cikin zuciya, Zai buɗe mana dukan gaskiya. 3) Ruhunka Yesu, Ruhunka kaɗai Zai tsarkake zukatanmu sarai. Ikonsa ne zai juye nufinmu, I, daga ƙeta zuwa Allahnmu. 4) Ruhun bangaskiya, Ruhun ƙauna kuwa, Ruhu Mai Tsarki, kyautar hannunka, Shi zo, shi sauko bisa dukanmu, Ikonsa kuwa shi zauna cikinmu.Fa' che piova Иисус печальным взором The Galilean Fishers Toil خد مكانك Chvalte Hospodina z nebes На нас излей Бог 我们乃主精兵 ЬОзгюрлюк Вар أحمدك يارب بين الشعوب يسوع أنت رفيقي
Song not available - connect to internet to try again?