1) Yabo ga Allahnmu, shi ne mahaliccin kome ! Ya raina, yabe shi, shi ne Mai Ceto, mai kiwo. Zo, masu ji, Maza da mata ku zo, Ku guso nan, ku yabe shi. 2) Yabo ga Allahnmu, mai mulkin Sama da duniya! Ya kiyaye mu ƙarƙashin fukafukan kansa. Ba ka ji ba? Bukatar kowa ya biya Ta wurin ikon ƙaunarsa. 3) Yabo ga Allahnmu, wanda ya tsare mu duka ! Kullum jinƙai da alheri su kan kiyaye mu. Lura da kyau. Kome Mai Iko ya iya, Don ƙaunarsa a gare mu. 4) Ya raina duka, ka yabi Ubangiji Allah. Yara da manya ku zo a gabansa da waƙa. Bari "Amin" Shi fito bakinmu duk. Har abada mu yabe shi.Why Don't You Let Go Di Saat Malam Sunyi Sepi BEN BİR KULUM Սա Իմ Սիրո Երգն է Bóg wierny słowom Swym Худовандо, дили мо шод аз Ту wǒ men yào cháng xǐ lè ربي اجعل في صلاتي حياة Мен Сендей болғым келеді О, Иса Доноликнинг Йўли
Song not available - connect to internet to try again?