1) Yanzu, ya Uba, muna tunawa Da ƙaunarka mai kawo fansarmu. Sabili da jinƙanka mai yawa, Mun zo ta wurin Matsakancinmu, Wanda ya ba da kansa dominmu Domin ya fanshi dukan zukata. 2) Ya Uba, duba fuskar Almasihu, Ka sa a iske mu a cikinsa . Kada ka duba kasawarmu dai, Mu masu ƙanƙantar bangaskiya. Gama shaidar cetonmu mu ke yi Daga laifofinmu da hakkinsu. 3) Ka ji addu'armu da za mu yi Sabili da masoya, ƴanuwa, Ka kare su dai daga hatsari, Ka kiyaye su cikin lafiya Ka ba su nasara a duniya, Su zama naka fa har abada. 4) Mu ma mun zo mu amsa kiranka, Ya Yesu mai ƙauna ba iyaka. Ta wurin jinƙanka da jininka, Ka cece mu duk daga mugunta. Ka karƃe mu mu zama bayinka, Ka sa mu zauna kullum cikinka.Гелин О'на Тапалъм Ty nám dávaš dary Полетели в высь Oh dichosos y bienaventurados Зинджирлери Кърмак على جناح النسمة Амьд үг Pojď nyní je čas Знаешь ли идя здесь по пути Бундан Биле
Song not available - connect to internet to try again?