1) Yaƙi 'na nan, yaƙi na Almasihu ne, Ku Masu Bi, yi shirin yaƙin nan. Ubangijinmu shi ne sarkin yaƙin nan Da mu ke yi, zai ba mu nasara. KORUS Yaƙi 'na nan, ku Masu Binsa, Ku nemo kayan yaƙin nan, Sulken adalci, kwalkwalin ceto, Da garkuwa ta bangaskiya, Takalma na shirin bishara, Gaskiya ce ɗamararmu, Takobin Ruhu--Maganar Allah, Da su mu ke yin nasara. 2) Ku ƙarfafa a cikin Ubangijinmu, Ku tsaya fa ta wurin bangaskiya. Kokawarmu tare da Shaiɗan ne da Ikoki nasa da kuma zunubi. Korus 3) Ku yi aniya, ga Yesu yana zuwa Don ya dube mu a cikin yaƙin nan. Ga shi, hakkinsa yana nan tare da shi, Zai bayar wa masu cin nasara. KorusZ mych tysięcy godzin życia sbḥwh sbḥwh ṣlạẗ ạlfqyr ṣwt yswʿ Сенімен кім теңелер سأشدو حباً لإلهي จงยินดีอยู่เสมอ باعىنامىن ạlkẖṭyẗ Моя душа беспомощна
Song not available - connect to internet to try again?