1) Yesu, Ɗan Allah, Mai Ceto ne, shi za ya tsare ka. Yesu mai taimakonka ne, shi za ya tsare ka. KORUS Yesu zai tsare ka ko wane gu, ko wace sa'a. Yesu zai tsare ka, Yesu zai tsare ka. 2) Yesu ya mutu don laifinka, shi za ya tsare ka. Zunubai duka ya ɗauke su, shi za ya tsare ka. Korus 3) Yesu kuwa ya fito kabarin, shi za ya tsare ka. Shi ne mai rai har abada, shi za ya tsare ka. Korus 4) Idan jaraba ke damunka, Yesu zai tsare ka. Ikonsa ba za ya kare ba, Yesu zai tsare ka. Korus 5) Lokacin ciwo fa yana nan, shi za ya tsare ka. Shi ne mai warkarwa ba mai fi, shi za ya tsare ka. Korus 6) Kada ka ji tsoron kome dai, shi za ya tsare ka. Sama da duniya nasa ne, shi za ya tsare ka. KorusМен билан бўлгин Я співаю як Спаситель Минует лето и для нас Ich brauch dich allezeit FOLLOW ON ! ạ̉btạh yạ ạ̉btạh Mahkota Duri yang Kejam أنا ماشي ولي معاك 圣灵带着你我走 Когда сгустились краски
Song not available - connect to internet to try again?