1) Yesu gaban Kayafas, Yesu gaban mayan malamai, Yesu gaban Bilatus, domin ya fanshe ni. An yi masa bulala, an yi masa ba'a, Yesu ya sha wahala, domin ya cece ni. KORUS Yesu ya sha wahala (3x) Domin ya fanshe ni. 2) An tofa masa miyau, da babbakun magana. Yesu ya ɗauki giciye domin ya fanshe ni. Yesu a bisa giciye, ya zub-da jininsa, Yesu a cikin Kabari, domin ya cece ni. Korus 3) Yesun mu ya tashi da rai, Yesun mu yana da rai Yesu ya hau cikin sama Domin mu sami rai 4) Ka tuna domin ran dawowarsa Gama ranar nan ƙarshe ne. Bass : "Ƙarshe ne" Ƙarshe ne, ƙarshe ne, Gama ranan na ƙarshe ne. Korus 5) Ka tuna da miyagun ayyukanka daina su Kamin Yesu ya dawo. Bass:"A ƙarshe Ayyukan miyagu, ka daina su Kamin Yesu ya dawo. Korus 6) Ka tuna randa za ka Kabari Gama ranan nan ƙarshe ne. Ƙarshe ne, ƙarshe ne Ran da za ka Kabari, ƙarshe ne. KorusSpirit Move Over Me Чармъха Бакън Во Христе я всё смогу klạm ạlrb ynyr Hiç görmedi insan güozü Il Tuo grande amore اسمان تىرەيت توولورۇ قىرعىزىمدىن 这是一个争战的日子 Choć na naszej drodze Их Эзэнээ би бүх
Song not available - connect to internet to try again?