1) Yesu Kristi yana zuwa don ya ɗauki masu bi Bar mu kasance da shiri, fitilinmu suna ci Wanda ya yi shiri duka zai tafi tare da shi Yesu yana dawowa a duniya. KORUS Yesu yana dawowa a duniyan nan Don ya fyauci masu bi, Ya kai su can. Ka yi shiri fa mai bi, ka daidaita tafiyarka, Yesu yana dawowa a duniya. 2) Duba ango yana zuwa, ba labari, ba zato Ranan nan ba sauran tuba, ba kuwa wani taimako. Kada dai ka yi jinkiri har Ubangiji ya zo. Yesu yana dawowa a duniya. Korus 3) Wanda ba ya karɓi Yesu ba zai shiga damuwa, Babu sauran shirin kome, babu sauran gafara. Kai da ka ke ƙin Mai Ceto, rabonka sai balaka Yesu yana dawowa a duniya. Korus 4) Can a sama Gidan Allah, yawan daɗi za mu ji Muna nan tare da Yesu, muna hutawa da shi Babu sauran ɓacin zuciya, babu sauran a zunubi Yesu yana dawowa a duniya. KorusАФФЕТ АФФЕТ АЛЛАХЪМ 回首再回首 Ciemne się chmury piętrzą Jesus lever, graven Quante volte sai... wsṭ ạltjạrb yạ fạdy ạ̉nạ ậty ạ̹lyk أنا عايزك إنت wǒ shǔ zhǔ Благославяме Те, Господи
Song not available - connect to internet to try again?