1) Yesu, maganar rai, lura da ni. Nan cikin duniya ga zunubi. Shaiɗan da wayonsa ya ruɗe ni, Zo nan da ikonka, ka cece ni. 2) Yesu, mai fansar rai, ka wanke ni Da jinin sadaka mai tsarki. Tun da ka ba da rai saboda ni, Jawo ni wurinka, ka riƙe ni. 3) Yesu, gurasar rai, ba ni in ci Yadda ka bayar da a Galili. Ba ni da kome nan sai kai kaɗai, Kullum ka cishe ni da jibin rai. 4) Yesu, mai ba da rai, tuna da ni. Alherin halinka ya gamshc ni. Zubo da Ruhunka, tsabtad da ni, Har zan yi nasara da zunubi.متكلي أنت Toate valurile lumii au lovit corabia ta Ne teď พระเจ้าพระบิดา yé sū shì zhǔ Tek Másihte úmittenem La pace e l'amore di Gesù رفعت عيني Sevinç sạ̉gẖny byn ạlnạs
Song not available - connect to internet to try again?