1) Yesu mu ne naka, kai ka saye mu, Ga kuwa muna zuwa bayanka yanzu. Inda za ka duka, wurin za mu bi, Kome wuyar aiki, lalle za mu yi. Kome ya same mu, ko a cikin rai, Ko ya kai ga mutuwa, Yesu mu ke bi. 2) Masu Bi, ku tashi, yi da zuciyarku, Aikin Ubangiji yana jiranku. Ga mutanen duniya, duhu su ke bi, Ba sa bin tafarki, ƙaƙa za mu yi ? Lalle sai mu tashi, hutu sai mu ƙi, Har labarin Yesu dukansu sun ji. 3) Duba can a Sama, ga mazuninmu, Daraja da tsarki, ba misalinsu. Babu saura kewa, babu rabuwa, Babu sauran cuta, babu mutuwa. Gaba dai, ƴanuwanmu, yad da duniya, Sama mu k enema, gidan tsarkaka. 4) Kome daɗin Sama, wanna ne mai fi, Yesu za mu gani, Yesu za mu ji. Ƙafa, hannu, goshi, shaida su ke yi Da azabar kansa fansarmu ya yi. Sauri fa, jama'a, babu hutawa! Yesu mu ke nema, za mu wurinsa.Еһтијаҹым вар İsa yoldaşımız Құтқардың мені Иса 自然界美景 ما أمجد الحبيب Йюдже Раб, Сана Тапънъйорум Алаканыңа ачылган, өмүрүмдү мен тапшырам Con Te Мәдһийилә, мәдһийилә Самавийни مين اللي قال
Song not available - connect to internet to try again?