1) Yesu, na naɗa ka a cikin zuciyata. Ba wani iko ko'ina sai naka, Sarkina. Kai yaro ne a da tare da mu ka sha Jaraba, kai Mai Nasara, Yesu Mai Cetona. 2) Yesu, na naɗa ka a cikin zuciyata. Ba wani wanda na ke so shi amshi mulkinta Da zunubi kaɗai ya cika nawa rai, Amma yanzu na sani kai Ubangijina ne. 3) Yesu, na naɗa ka, ban rage kome ba, A bisa nawa duk da ni, sarauta za ka yi. Da goshinka ya sha azabar naɗin ƙaya, Yanzu ka ratsa mutuwa, ya kai Mai Nasara! 4) Yesu, an naɗa ka domin biyayyarka. Suna mafifici aka ba mai mulkin mutuwa. Yesu, ka cancanci ƙauna madauwamiya. An naɗa ka! An naɗa ka tun da har abada! 5) Allah ya naɗa ka Ɗansa Maɗaukaki. Baki ya kasa furtawa labarin girmanka. Gare ka ɗaukaka har abada, Amin An naɗa ka! An naɗa ka! Immanuel Almasihu.In Ka Karanta Cikin Matta Fa Любовь в сердце отца Tuhan, Kasihanilah 一起完成大使命 Oh Cristo en tu muerte Open Skies Sən mənim Göylərdə olan Atamsan For Your Glory (Send the Winds) ЧЫККАН КӰНИҤЛЕ, КУДАЙЫМ Miposaka ny vonjy
Song not available - connect to internet to try again?